Mayakan Kurdawa na cigaba da dakatar da yunkurin mayakan ISIL na kame garin Kobani dake Syria, amma ana cigaba ta tafka mummunan fada a garin dake kusa da bakin iyakar Turkiyya.
Rundunar Sojin Amurka tace jiragen yakinta na sama, tare da na Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa sun kai hare-haren sama guda uku Asabar dinnan da kuma Lahadi a Kobani, inda suka yi nasarar lalata shingar mayakan sa kai, da inda suke shirye-shiryen yaki
Kungiyar lura da hakkin bil adama a Syria dake Britaniya tace mayakan sa kan na samun rashe-rashen rayuka da yawa a wannan fa
Sakatare Janar na MDD Ban Ki moon yace “dubban rayukan jama’a ne suke cikin hadari” sanadiyar yunkurin kame Kobani, inda ma Yayi kira ga bangarorin dake hamayya akan “su kiyaye kashe-kashen fararen hula, da cin mutuncinsu.”
An ga hayaki mai duhu a samaniyar birnin Kobani Lahadinnan yayin da mayakan Kurdawa suke cigaba da kokarin kare shi daga farmakin mayakan sa kai na ISIL.