Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Saudiyya Ta Zartar Da Hukuncin Kisa Ga Mutane 47


Hoton Fastar Shehin 'Yan Shi'a Nimr al-Nimr
Hoton Fastar Shehin 'Yan Shi'a Nimr al-Nimr

Gwamnatin kasar Saudiyya ta yanke hukuncin kisa ga wasu mutane 47 ciki har da wani Shehin Malamin 'yan Shia mai suna Nimr al-Nimr.

Kakakin Gwamnatin Saudiyya Mansour Ben Turki, ya jaddada cewa an hukuncin kisan mutanen da suka kashe bisa adalci. Yace guda 43 daga cikin 47 suna da hannu dumu-dumu a daukar rayuka da dama, an kuma kashesu gaban shaidu da likita.

Ministan harkokin cikin gidan kasar Saudiyya ya sanar da kisan a safiyar yau bisa zarginsu da ayyukan ta’addanci, ciki har da wani fitaccen Malamin Shia mai suna Sheikh Nimr al-Nimr.

Wannan malamin na cikin wadanda suka zama a sahun gaba wajen yin zanga-zangar da ta haifar da guguwar sauyi a kasashen Larabawa a shekarar 2011.

Manyan Malaman ‘yan Shi’ar kasashe kamar su Lebanon da Iran sunce wannan kisa na iya barin baya da kura. Kungiyar rajin kare ‘yancin bil’adama ta Amnesty tace Saudiyya ta fi kowace kasa yankewa mutane hukuncin kisa in ka dauke kasar Sin da Iran.

XS
SM
MD
LG