Majalisar dokokin kasar Iran ta bayar da sanarwa a yau talata tana yin tur da kashe "daruruwan" 'yan mazhabin Shi'a da sojojin Najeriya suka yi a garin Zariya dake Jihar Kaduna a arewacin kasar.
Kamfanin dillancin labaran gwamnatin Iran, IRNA, ya ce a lokacin da aka bude zaman majalisar a yau talata, wakilai 214 daga cikin wakilai 290 na majalisar sun dora laifin tashe-tashen hankulan a kan sojojin Najeriya.
'Yan majalisar dokokin ta Najeriya sun yi kira ga shugaban Najeriya da ya kafa wani kwamiti na musamman da zai binciko wannan lamarin.
Wannan yana zuwa a daidai lokacin da daya daga cikin manyan shaihunan malaman Shi'a na duniya, babban Ayatollah Lotfollah Safi Golpaygani, yake nuna matukar damuwa da kashe-kashen tare da yin kira ga hukumomi na duniya da su yi tur da irin wadannan kashe kashen.
Marja Ayatollah Golpaygani yace maimakon su maida hankulansu wajen kashe 'yan ta'addar Boko Haram, sojojin Najeriya sun gwammace su kashe 'yan Shi'a dake fuskantar danniya, kuma ba su yin barazana ga wata kasa ba.
Har yanzu dai ba a ji ta bakin hukumomin Najeriya a kan wannan suka ta kasar Iran ba.