Firayim-Ministar Britaniya, Theresa May ta fada a yau Lahadi cewa mutanen da suka kai hare-hare guda ukku akan kasarta a cikin wattani ukku da suka gabata, wadanda suka hada da hare-haren da aka kai yau Lahadi akan Gadar London da Kasuwar Borough, mutane dake da akidar “muguwar dabi’a da kuma akidar Islama mai tsanani.”
Firayim Minista May tace mutanen kasarta sun cika hakurewa akidar ra’ayi mai tsanani, inda ta kara da yin kira akan daukar matakin shawo kan matsalar.
‘Yansandan birnin na London sun ce mutane bakwai da kuma su maharan guda ukku suka mutu acikin wannan farmakin na baya-bayan nan, yayinda wasu mutane 48 suka sami raunukka, wasunsu masu tsanani sosai.
Hukumomi sunce yanzu haka ma’aikatan tsaro na can suna kai samame a wasu unguwanni dake gabascin birnin London, dangane da hare-haren baya-bayan nan, koda yake ba’a bada karin haske kan ainihin abinda ke faruwa ba.
Wannan al’amarin na baya-bayan nan dai ya soma ne daga misalin karfe 10 na daren jiya Assabar lokacinda wasu suka tuku wata mota cikin matsanancin gudu zuwa kan gadar ta London, daga baya motar ta juya zuwa Kasuwar Borough inda mutane ukku suka fito daga motar, suka soma sukar mutane da wukake.
Mintoci takwas bayan soma harin, ‘yan sanda suka bindige maharan ukku har Lahira.
Facebook Forum