Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Rajin Kare Muhalli A Nahiyar Afirka Sun Ce Afirka Zata Ga Illar Fitar Amurka Daga Yarjejeniyar Paris


Africa Action Summit Morocco
Africa Action Summit Morocco

Kasan cewar mafiya yawan al'ummar Afirka manoma ne sauyin yanayi zai fi shafarsu, inji masu raji kan yaki da dumamar yanayi na yankin

A halin da ake ciki, ‘yan rajin kare muhalli a nahiyar Afirka sun ce shawarar shugaba Donald Trump ta janyewa daga Yarjejeniyar Dakile Sauyin Yanayi ta Paris zata iya yin illa ga nahiyar.

Shugaban sashen tsara manufa na Asusun Kula da Namun daji ta Duniya a Afirka ta Kudu, Saliem Fakir, ya bayyana damuwa a kan kudi Dala miliyan dubu 2 da ya kamata Amurka ta bayar gudumawa karkashin yarjejeniyar, ga wani asusun tallafawa kasashe masu tasowa wajen daukar sabbin dabaru da fasahar ceton yanayi.

Fakir yace da yake akasarin mutanen Afirka manoma ne, sauyin yanayi zai fi shafarsu, kamar karuwar zafi da rashin wadataccen ruwan sama.

Su ma shugabannin Afirka sun bayyana bacin ransu da wannan shawara ta Trump.

Shugaba John Dramani Mahama na kasar Ghana, ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa, “Tunani na a nan shine Amurka ta kau da kanta daga jagoranci kan wani batun dake da matukar muhimmanci ga duniya.”

Ita ma gwamnatin Afirka ta Kudu ta fito da kakkausar harshe tana sukar lamirin wannan mataki na Amurka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG