Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sami Gawarwakin 'Yan Bindigar Da Sukayi Fashi A Gidan Caca A Manila dake Philippines


Yan Bindiga sun cinnawa gidan caca wuta wanda yayi sanadiyyar mutuwar kimanin mutane 36 a Manila Babban birnin Philippines.

Jami’ai a Philippines sunce Yan bindiga sun afkawa wani gidan caca a babban birnin kasar, Manila inda suka cinnawa teburan caca wuta a wajen da yake makare da mutane, wanda ya jawo hayaki ya turnuke wajen har yayi sanadiyyar mutuwar mutane 36.

Yan bindigar sun cika jakar goyawa a baya da sulallan cacar kafin su gudu amma an gano su a mace a hotel din da yake makwabtaka da gidan cacar a yau juma’a alamarin da akewa kallon kisan kansu.

Jami’in 'yansandar birnin Manila Chief Oscar Albayalde yace jami’an aikin kashe gobara ne suka sami gawarwakin su a cikin dakin da hayaki ya cika sakamakon hayakin da suka shaka. Babu wanda yake da alamar harbi a cikinsu.

Harin ya sa daruruwan mutane gudu cikin dare a wajen wurin shakatawar mai suna World Manila Complex. Mutane da yawa sunji raunuka a kokarin tserewa.

Yan sanda sun tabbatar da babu wata alama da ta nuna aikin ta’addanci ne.

Da fari Jami’ai sun ce sun yarda da Fashi ne dalilin aika aikar. Masu Magana da Turanci da ake zargi sun kwashi kimanin Pesos miliyan 113 wanda yayi daidai da Dalar Amurka $226,000 na sulallan caca, wadanda aka samu a cikin jakunkunan da aka gano.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG