Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Mutanen Kasar Lesotho Ke Zaben 'Yan Majalisar Dokoki


Jam’iyyun siyasa fiyeda 30 ne suka tsaida ‘yan takara amma ana jin karshenta zaben zai kasance tsakanin manyan jam’iyyun siyasar kasar guda biyu,

A yau ne mutanen kasar Lesotho ke gudanarda babban zaben wakilan majalisar su ta dokoki, da fatar cewa wadanda zasu zaba zasu iya cika musu alkawurran da aka yi na inganta musu rayuwa a baya, aka kasa cikawa,

Daga cikin manyan bukatun da suke fatar ganin sababbin shugabannain sun biya ba kamar samar da ruwan sha, lantarki, ilmi da kiyon lafiya, tareda samarda aiyukkan yi ga jama’a.

Zaben na yau shine zabe na ukku irinsa da ake gudanarwa a Lesotho din a cikin shekaru biyar da suka gabata.

Kuma ana zaben ne a sanadin kuri’ar rashin amincewa da gwamnatin kasar ne da aka jefa a watan Maris da ya wuce, abinda ya sa gwamnatin ta nemi a shirya zaben, maimakon tayi murabus, har ragamar ta koma hannun ‘yan adawa.

Duk da cewa jam’iyyun siyasa fiyeda 30 suka tsaida ‘yan takara a gundumomi kamar 80, ana jin karshenta zaben zai kasance ne a tsakanin manyan jam’iyyun siyasar kasar guda biyu, wadanda tun 2012 suke ta gwagwarmaya da juna na fagen zabbukka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG