Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Indonesia: Wani Jirgin Sama Na Soji Ya Ci Karo da Otel


Wurinda jirgin saman ya rikito bayan da ya ci karo da wani otel
Wurinda jirgin saman ya rikito bayan da ya ci karo da wani otel

Jami’an kasar Indoneshiya sun fadi cewa akalla mutane 49 sun mutu yayinda wani jirgin sufirin sojan kasar ya fado a kan wata unguwa dake tsibirin Sumatra

Jirgin, samfurin Hercules C-130, yayi kokarin juyawa ya koma tashar saukar jiragen sama bayan da ya tashi yau Talata, sai ya kara da wani otel da wasu gidaje guda 2 a Medan, birni na 3 mafi girma a Indoneshiya.

Hotuna daga kafafen sada zumunci sun nuna jirgin da ya fadi yana ci da wuta, da kuma yadda hayaki daga gidaje da motocin da suka lalace ya turnuke wurin.

Ana sa ran adadin wadanda suka mutu din zai hau. Kafafen yada labarai da jami’ai na wannan birni sun ce mutane kusan 113 ke cikin jirgin sojan na Indoneshiya. Babu tabbacin ko mutane nawa ne takamaimai suka mutu a kasa ko kuma suka jikkata sanadiyar faduwar jirgin.

Wani mai Magana da yawun rundunar sojan kasar yace, jirgin ya fadi ne ‘yan mintoci bayan da ya tashi daga wata tashar sauka- da -tashin jirage da ke kusa da wurin. Wata Kafar yada labaran birnin kuma tace jirgin yayi kokarin juyawa saboda wasu matsalolin na’ura da ya fuskanta amma dai ba’a fayyacesu ba.

Rundunar sojan Indoneshiya ta sha fuskantar munanan faduwar jiragen sama a cikin ‘yan shekarun nan, ciki har da na watan Yunin shakarar 2012, lokacin da wani jirgi ya fada a wani gini a Jakarta, ya kashe mutane 11.

XS
SM
MD
LG