Hukumomi a kasar Indonesia sun tabbatar da aiwatar da hukuncin kisa akan wasu mutane takwas da aka samu da laifin safarar miyagun kwayoyi, ciki har da mutanen kasashen waje guda bakwai, lamarin da ya janyo kakkausar suka daga kasashen duniya da dama.
An dai kashe mutanen ta hanyar harbi, kamar yadda Attorney Janar din kasar Janar Muhammad Prasetyo ya bayyana, wanda kuma yace hakan zai kare kasar daga fadawa cikin matsalar miyagun kwayoyi.
A cewarsa, an aiwatar da hukuncin ne da karfe biyar da rabi da minti biyar agogon Birtaniya, an kuma bayyana mutuwarsu bayan mintuna talatin, ya kuma ce an yi harbin a cikin kwarewa.
Ya kara da cewa aiwatar da hukuncin kisa ba abu ne mai dadi ba, amma domin a kare kasar daga fadawa cikin hadari, ya zama dole a aiwatar da wannan hukunci.
Daga mutanen da aka aiwatar da hukuncin a kansu, akwai ‘yan Najeriya guda hudu, ‘yan kasar Australia guda biyu da wani dan kasar Brazil guda daya, sannan sai wani dan kasar ta Indonesia guda daya. An aiwatar da hukuncin ne a wani gidan yari da ke cikin daji mai suna Nusakambangan a tsakiyar yankin Java.