Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Idris Guda Na Wikki Tourist Ya Yaba Da Baba Ganaru


Idris Guda
Idris Guda

Dan wasan tsakiya na gefe na Kungiyar kwallon kafa ta Wikki Tourist, dake Garin Bauchi, a tarayyar Najeriya Mohammad Idris Guda, ya yabawa sabon Mai horas da Kungiyar kwallon kafa ta Wikki, Moh'd Baba Ganaru bisa kokarin da yakeyi na ganin Kungiyar ta cigaba a fagen wasan kwallon kafa.

Idris Guda, yace yanada kwarin gwiwar Kungiyarsu ta Wikki, zata taka rawar gani fiye da shekarun baya karkashin jagoranci Baba Ganaru.

Ya kuma kara da cewar a wannan karon zai kara damara wajan zurara kwallaye a raga a wasan firimiya lig na kasa da kuma wasannin da Wikki, zata wakilci Najeriya na cin kofin zakarun kasashen Afirka CAF Confederation Cup 2017.

Ranar 12 ga watan fafurairu na wannan shekarar 2017, Kungiyar ta Wikki, zata yi tattaki zuwa kasar Sierra Leone, don fara fafatawa a wasan na CAF.

Muhammad Guda ya jefa kwallonsa ta farko a wannan kakar wasan a wasan da Kungiyarsa tayi tsakaninta da Ifeanyi Ubah, a Bauchi, a mako na hudu na gasar firimiyar bana inda Wikki, suka samu nasara da kwallaye 3-1.

Wikki Tourist, dai tana mataki na takwas a gasar firimiyar bana mako na hudu, Idris yayi kira ga takwarorinsa ‘yan wasa da su bada goyan baya ga sabon kocin Ganaru, domin ciyar da Kungiyar gaba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:39 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG