A cigaba da gasar firimiya lig da ake yi a kasar Ingila, ta shekarar 2016/2017, mako na ashirin da uku, yau Kungiyar kwallon kafa ta Bournemouth, zata fafata da Crystal palace. Arsenal zata karbi bakuncin Watford, Burnley kuwa zasu gwabza da Leicester City.
Har ila yau kungiyar MiddleBrough zata kara da Westbromwich, Sunderland da Tottenham, Swansea City zasu barje gumi da Southampton, Liverpool kuwa zata kece rainine da Chelsea.
Za'a fara wasu wasanninne da misalin karfe tara saura kwata agogon Najeriya Nijar kamaru da kasar Chadi.
Shi kuwa Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Antonio Conte, ya gargadi 'yan wasansa da su zage damtsee domin ganin sun lashe gasar firimiya ta bana, Conte, yace kar suyi La'akari da cewa suna saman tebur domin komai na iya kasancewa in har basu kare matsayinsu a na daya ba.
Chelsea dai ita take jan ragamar teburin firimiya a yanzu haka da maki 55 inda ta ba mai biyemata maki 8, yayinda Arsenal, ke mataki na biyu da maki 47
A yau dai Chelsea zata kara da Liverpool, wanda take mataki na hudu da maki 45
A filin wasa na Anfield da misalin karfe tara na dare agogon Najeriya da Chadi. A sha kallo lafiya.