A bayan zama da hukamar kula da wasan kwallon kafa ta kasar Ingila FA tayi bisa tuhumar da takeyi wa mai horar da ‘yan wasan Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Arsene Wenger.
Hukumar a hukuncin da ta yanke masa ta hana shi hawa kan layi ko kuma zama a bencin kungiyar a lokutan wasani har hudu, da kuma cin sha tarar fam dubu £25.
Hukumar tace ta kama shine da laifin cinzarafin mataimakin alkalin wasa na 4 a Yayin wasan da Kungiyar Arsenal, tayi da Burnley a gasar firimiya lig 2016/2017 mako na 22 inda ta doke Burnley kwallaye 2-1.
Bayan haka a cigaba da wasannin FA Cup 2016/2017 da akeyi an fafata wasanni da dama, Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta Sha kashi a hannun Wolverhampton daci 2-1, Tottenham ta doke Wycombe wandered daci 4-2, Crystal palace bata ji da dadiba a hannun Manchester City daci 3-0 Oxford United ta lallasa Newcastle United daci 3-0.
Chelsea ta doke Brentford 4-0, Burnley ta samu nasara akan Bristol City da kwallo 2-0, Lincoin City na da 3 Brighton & Hove nada 1
Arsenal ta lallasa Southampton kwallaye 5-0, Millwall ta casa Watford da kwallo 1-0 .
Fulham ta samu nasaran doke Hull City da ci 4-1, Sutton United 1-0 Leeds, Manchester United ta doke Wigan Athletic da kwallaye 4-0.