Babban kocin kungiyar kwallon kafa ta Najeriya super Eagles, Gernot Rohr, ya bayyana damuwarsa akan kasancewar wahala da bata lokacin da kungiyar ke fuskanta wajan samarwa ‘yan Najeriya haifaffun kasashen waje masu taka leda Fasfo ko kuma takardar izinin shiga Najeriya.
Jagoran kungiyar yayi shawagi ciki da kewayen nahiyar turai domin nemo ‘yan asalin kasar da aka Haifa a wasu kasashe musamman kwararru a wasan tamaula domin gayyato su zuwa kasar su marawa kungiyar baya wajan taka leda a wasanninta na nan gaba.
Gernot ya bayyana cewa sunan dan asalin Najeriyar nan haifaffen kasar Jamus, Brian Idowu, yayi batan dabo a cikin jerin sunayen ‘yan wasan da zasu takawa kasar leda a wasannin cin kofin duniya na shekarar 2018, a sakamakon matsalar Fasfo.
A cewar sa, an fada masa cewar babu wata matsala wajan samun Fasfo din Najeriya, bai kamata ya dauki lokaci mai tsawo ba, amma ya fahimci cewa ba haka lamarin yake ba a yawancin lokuta.