Haka kuma rahotannin safiyar yau Juma’a na cewa Janar Tiani ya tsige mashawarcinsa na musamman a fannin man fetur Maman Lawan Gaya, wanda dama wasu ‘yan kasar sun sha korafi dangane da abin da suka kira cuwa-cuwar da ke tattare da hada-hadar mai a kasar, lamarin da suke ganin yana bukatar gudanar da bincike.
A cikin daren 13 wayewar 14 ga watan Janairun 2025 jami’an tsaro suka kutsa gidan tsohon ministan man fetur Moustapha Barke da ke birnin Yamai inda bayan gudanar da bincike suka yi awon gaba da shi.
Kawo yanzu, wato wuni na 3 da faruwar al’amarin, iyalinsa da makusanta ba su da masaniya game da inda aka tafi da shi, haka kuma ba wani bayani daga bangaren hukumomi dangane da dalilan cafke tsohon ministan.
Moustapha Barke na daga cikin mambobin gwamnatin da soja suka kafa makwanni kadan bayan kifar da tsohon shugaba Mohamed Bazoum a watan Yulin 2023.
An tsige shi daga mukaminsa a watan Agustan 2024 tun a ranar faruwar abin aka yi ta yada jita-jitar cewa matakin na da nasaba da wata cuwa-cuwa mai alaka da bada lasisi ko kwangilar ayyukan hakar albarkatun karkashin kasa.
Amma har izuwa yau hukumomi ba su fadi dalilin daukan matakin ba, sai dai kakakin kungiyar FPSN Bana Ibrahim na cewa za ta yiwu abubuwan da ake zargin sun wakana a zamanin da yake rike da mukamin gwamnati ne mafarin haka.
A yayin da labarin kama tsohon ministan CNSP ke daukan hankulan jama’a, sai kuma aka sami labarin cewa shugaban gwamnatin mulkin sojan Janar Abdourahamne Tiani ya tsige mai ba shi shawara na musamman a fannin man fetur Mahaman Lawan Gaya.
Da ma tun ba yau ba ‘yan fafutika ke kiraye-kirayen ganin an dauki matakin daidaita lamura a sha’anin gudanar da arzikin karkashin kasa fannin da ake zargin cin hanci ya yi wa katutu.
Saboda haka shugaban gamayyar kungiyoyin yaki da cin hanci wato RNAC Adamou Oumarou ke sake nanata kira.
A ranakun farkon karbe madafi hukumomin mulkin sojan Nijar sun kudiri aniyar sauya abubuwa a harkokin ma’adinan karkashin kasa ta yadda wannan arziki da Allah ya hore waka kasar zai amfani jama’arta injisu.
Matakin da a halin yanzu ya janyo kwace wa Orano na Faransa da Goviex na Canada lasisin hakar uranium.
Haka kuma zargin ‘yan China da durba-durba ya sa hukumomi dakatar da aika danyen mai daga rijiyoyin Agadem zuwa tashar jirgin ruwan Cotonou a watan Yunin 2024 kafin daga bisani al’amura su daidaita.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:
Dandalin Mu Tattauna