Jamhuriyar Nijar da kamfanin WAPCO - Nijar (West African Oil Pipeline Company), sun rattaba hannu domin samar da tsaro ga aikin hakowa, sarrafawa da ma jigilar man fetur a kasar ta Nijar.
Bututun man tsawonsa ya kai sama da kilomita dubu biyu daga Nijar har zuwa kasar Benin.
Wannan yarjejeniyar, tana la'akkari da hare-haren da a ke kai wa bututun man kasar, inda ko a karshen makon jiya, wadansu ‘yan ta'adda sun kai hari a yankin Yaya-Muntseika sannan suka arce zuwa Najeriya.
Sannan a farkon watan Disambar shekarar da ta gabata, jami'an tsaro 3 na kasar Benin daga cikin masu kula da bututun man sun hallaka a hannun ‘yan ta'adda a wajen Mallaville.
Kasar China za ta taimaka da jirage mara matuka, da kumbo, da ma taurarun dan adam na hango makiya daga nesa domin kare wannan bututu na Nijar.
Wannan yarjejeniyar dai tsakanin China da Nijar, za ta kawo karshen hare-haren da a ke kai wa kayayyakin ayyukan fetur a Nijar, tare da kare muradun kasashen biyu a wannan fannin na kasar.
Saurari cikakken rahoto daga Harouna Mamman Bako:
Dandalin Mu Tattauna