Tun ranar 23 ga watan da ya gabata ne hukumomi suka kama shugaban M62 Abdoulaye Saidou, jim kadan bayan kammala zaman shari’ar dake tsakanin kungiyarsa da gwamnatin Nijer a bisa zarginsa da hannu a mutuwar fararen hula a mahakar zinaren Tamou.
Chaibou Moussa, shine lauyan da ya shigar da kara ya ce sun sami bayanai dake tabbatar da cewa an cinnawa rumfunan wuta da gangan domin a daurawa jami’an tsaro laifi.
Amma a wani taron manema labarai da suka gudanar gamayyar kungiyoyin fararen hula CCAC, ta ce babu kanshin gaskiya a wannan zargi, tare da kira da a sake shi ya koma kan aikinsa na kare hakkin bil Adama.
Shugaban kungiyar MOJEN ta ‘yan rajin kare dimokaradiya Siraji Issa, ya gargadi takwarorinsa ‘yan fafutika su nisantar da kansu daga aikata abubuwan da ke kama da karan tsaye wa tsarin dimokradiya.
A karshen watan oktoban da ya gabata ne, jami’an tsaro suka yi luguden wuta a mahakar zinaren Tamou dake jihar Tilabery, lokacin da suka hango ‘yan ta’adda na kokarin boye makaman da suka sace bayan kashe wasu ‘yan sanda uku, lamarin da ya sa gamayyar M62 ta maka gwamnatin Nijer a kotu, a bisa zarginta da bada umurnin kisan gilla kan fararen hula.
Domin Karin bayani saurari rahotan Sule Muminu Barma: