NIAMEY, NIGER - Wannan ita ce dai hanyar da ‘yan ta’addar ke yi wa kansu guzurin abinci da sauran kayyakin bukatun yau da kullum, sai dai mazauna karkarar na ganin tsaurara matakan tsaro ita ce hanya daya tilo da za ta taimaka a murkushe aika-aikar da ake fama da ita.
Bayanai daga hukumomin tsaro sun yi nuni a game da yadda ‘yan bindiga a yankin Tilabery ke gudanar da harkokin saye da sayarwa a kasuwannin kauyukan gundumar Sanam da Abala Jihar Tilabery, wadanda suka hada da garin Ezza da Tamalawlaw da Abarey da Chimbarkawane da Tigzefan da Tamachi, dalili kenan ministan cikin gida ta hanyar shugabanin rundunonin tsaro ya umurci rufe wadanan kasuwanni har sai yadda hali ya yi.
A yankin Tahoua ma an gano cewa ‘yan bindiga na cin kasuwannin wasu kauyukan da ke iyakar Mali da Nijar lamarin da idan ba a gaggauta daukan mataki ba, na iya zama wata hanyar kara wa abokan gaba karfi mafarin rufe kasuwar kauyen Tebaram da Intakana da Inelou da Inabagargare, to sai dai wani mazaunin wannan yanki wanda ya so a sakaya sunansa saboda dalilan tsaro ya ce akwai wani hanzari ba gudu ba.
Jihar Tilabery da wani bangare na jihar Tahoua sun fada cikin yanayin tabarbarewar tsaro sanadiyar lalacewar al’amura a arewacin Mali a shekarar 2013, inda ‘yan ta’adda da barayi kan tsallako iyaka don satar dabobi karbar haraji har ma da kashe kashen fararen hula, abin da ya sa a shekarar 2017 hukumomin Nijar suka kafa dokar ta baci tare da hana sayar da man fetur da hana amfani da Babura a wuraren da matsalar ta yi tsanani.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma: