Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Nijar Sun Karyata Shirin Fille Kan Wasu 'Yan Kasar A Saudiya


Shugaban Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum
Shugaban Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum

Ma'aikatar harkokin wajen Nijar ta tabbatar da labarin kama wasu ' yan kasar a Saudiya dake dauke da miyagun kwayoyi. Sai dai kawo yanzu ba a yanke musu hukunci ba kuma ba a san makomar su ba a cewar hukumomi.

NIAMEY, NIGER - A wannan sanarwar ne sabanin yadda wasu masu amfani da kafafen sada zumunta suka yada cewa, a yau Juma'a ne za a fille wa wadannan matan kai kamar yadda tsarin shari'ar Saudiya ya yi tanadi.

Ta hanyar wata rubutacciyar sanarwa ne ofishin Ministan harakokin wajen Nijar ya yi karin haske dangane da labarin kama wasu 'yan kasar mata dauke da haramtattun abubuwa a kasar Saudiya.

Sanarwar ta tabbatar da cafke wadanan mutane amma kuma har I zuwa wannan lokaci ba a yanke musu hukunci ba sabanin yadda wasu majiyoyi ke cewa a wannan Juma'a 23 ga watan Ramadan na 1444, za a cire fille masu kai bisa tsarin shari'ar musulunci da ake zartarwa a Saudiya.

Wannan batu dake matukar daukan hankula a 'yan kwanakin nan ya janyo martanin jama'a da na masana shari’ar islama.

Sanarwar gwmanatin ta Nijar wacce ba ta fayyace yawan mutanen da Saudiyar ta kama ba, ba ta kuma yi bayani kan girma ko yawan abinda suka shiga kasa mai tsarki da shi ba, ta kara da cewa wadanda abin ya rutsa da su na samun ziyara a kai a kai a inda suke tsare a birnin Madina daga jami'an karamin ofishin jakadancin kasar a Jidda da ma danginsu.

Wasu ‘yan kasar na fatan ganin mahukuntan Nijar sun bi hanyoyin diflomasiya don ceto wadanan mata daga barazanar hukuncin kisa da suke fusknta.

A tsakiyar makon nan ne labarin kama wasu 'yan Nijar mata a Saudi Arabia dauke da myagun kwayoyi ya karade kafafen sada zumunta har ma wasu na ambatar sunaye da yada hotunan matan tare da bada tabbacin hukumomin kasa mai tsarki sun yanke hukuncin fille masu kai a wannan Juma'a 14 ga watan Afrilun 2023, amma kafin a wayi gari da sanarwar ma'aikatar harakkin wajen Nijar ta karyata wannan labari.

Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma:

Hukumomin Nijar Sun Karyatar Da Shirin Fille Kan Wasu 'Yan Kasar A Saudiya.MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:53 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG