Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar Ta Zama Ta Farko A Nahiyar Afirka Wajen Kawar Da Cutar Makantar Kuda

Nijar Ta Samu Nasarar Zama Ta Farko A Nahiyar Afirka Wajen Kawar Da Cutar Makantar Kuda
Nijar Ta Samu Nasarar Zama Ta Farko A Nahiyar Afirka Wajen Kawar Da Cutar Makantar Kuda

Hukumar kiwon lafiyar al’ummar Jamhuriyar Nijar ta ayyana samun nasarar kawar da cutar makantar kuda wato Onchocercose ko River Blindness daga kasar bayan fafutukar shekaru sama da 40.

NIAMEY, NIGER - Ministan kiwon lafiya Dr. Iliassou Idi Mainassara ya jagoranci bukin gabatar da rahoton binciken da ke nuna cewa kasar Nijar ta murkushe wannan cuta da a shekarun baya ta yi sanadin makancewar dubban mutane, abin da ke nufin ita ce kasa ta farko a nahiyar Afrika da ta samu irin wannan nasara.

Nijar Ta Samu Nasarar Zama Ta Farko A Nahiyar Afirka Wajen Kawar Da Cutar Makantar Kuda
Nijar Ta Samu Nasarar Zama Ta Farko A Nahiyar Afirka Wajen Kawar Da Cutar Makantar Kuda

Cutar makantar kuda da ake kira Onchocerchose ko kuma Onchocerciasis (ko River Blindness), cuta ce da wani nau'in kuda ke haddasa ta, wacce kuma ke shafar fata da idanun ‘dan adam a yankunan da Allah ya wadata da albarkatun ruwa.

A Nijar an yi fama da wannan masifa ne a yankunan gabar kogin Kwara kamar yadda shugaban shirin yaki da cutar onchocerchose Dr. Salissou Adamou Batchiri ya bayyana.

Nijar Ta Samu Nasarar Zama Ta Farko A Nahiyar Afirka Wajen Kawar Da Cutar Makantar Kuda
Nijar Ta Samu Nasarar Zama Ta Farko A Nahiyar Afirka Wajen Kawar Da Cutar Makantar Kuda
Nijar Ta Samu Nasarar Zama Ta Farko A Nahiyar Afirka Wajen Kawar Da Cutar Makantar Kuda
Nijar Ta Samu Nasarar Zama Ta Farko A Nahiyar Afirka Wajen Kawar Da Cutar Makantar Kuda

Lura da girman wannan matsala ya sa hukumomin lafiya suka bullo da wasu dabarun da suka bada damar samin mafita.

Bayan shafe shekaru na wannan yaki an gano cewa an kawar da cutar kwata-kwata daga kasar inji Ministan kiwon lafiya Dr Iliassou Idi Mainassara a yayin bukin gabatar da rahoton bincike.

Nijar Ta Samu Nasarar Zama Ta Farko A Nahiyar Afirka Wajen Kawar Da Cutar Makantar Kuda
Nijar Ta Samu Nasarar Zama Ta Farko A Nahiyar Afirka Wajen Kawar Da Cutar Makantar Kuda

Wakiliyar hukumar lafiya a Nijar Dr. Anya Blanche ta yaba da wannan aiki wanda a cewarta hukumar WHO ko OMS na daukansa da mahimmanci.

Ta ce bayanan da muka samu daga kwararun hukumar lafiya da suka bi diddigin yaki da wannan cuta sun yi nuni da cewa takardun da Nijar ta gabatar wa hukumar domin tantance sahihancin binciken da aka aiwatar sun sami karbuwa kuma nan gaba za a damka su a hannun kwamitin bincike mai zaman kansa domin tantance gaskiyar lamarin.

Nijar Ta Samu Nasarar Zama Ta Farko A Nahiyar Afirka Wajen Kawar Da Cutar Makantar Kuda
Nijar Ta Samu Nasarar Zama Ta Farko A Nahiyar Afirka Wajen Kawar Da Cutar Makantar Kuda

Hukumomin lafiya a nan cikin gida ta hanyar shirin yaki da cutar makantar kuda ko kuma Onchocercose sun kudiri aniyar ci gaba da ayyukan zuba ido a garuruwan kan iyakokin kasar don dakile dukkan wasu alamun sake bullar wannan masifa da ta makantar da dubban mutane a Jihohin Dosso da Tilabery.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Nijar Ta Zama Ta Farko A Nahiyar Afirka Wajen Kawar Da Cutar Makantar Kuda .MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:06 0:00

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG