Samar da kotunan daukaka kara a cikin manyan biranen jihohi Takwas tare da soke zaman shekar- shekara a jamhuriyar Nijer, na daga cikin irin matakan da gwamnatin kasar ta bayyana shirin dauka domin magance matsalolin shari’a.
Malam Nasiru Saidu, ya bayyana cewa talakawa na yawan koke koke akan yadda sai mutuum ya yi tafiya mai nisa kafin ya sami biyan bukata a bangaren shari’a, dan haka idan gwamnati ta kudiri aniyar kafa kotuna a wadannan jihohi, abu ne da talakawa zasu kara da hannu biyu.
Domin kusantar da kotunanj shari’a kusa da jama’ar karkara, gwamnati ta kudiri aniyar bude kotunan a yankunan karkara.
Dan majalisar dokokin kasa Malam Shitu Mammam, ya bayyana gamsuwa da matakin tare da shawartar hukumomi su dauki matakan amfani da na’urorin zamani wajan ayyukan bada takardu irin su takardun haihuwa a daukacin kotunan kasar ta Nijer.
Wakilin muryar Amurka a yamai Sule Mumuni Barma ya aiko mana Karin bayani.
Facebook Forum