Girgizar kasa mai karfin maki 5 d a digo bakwai ta afkawa kasar Tanzania a yankin da ake kira Great lakes da turanci Asabar din nan, ta halaka akalla mutane 10, ta rusa gine gine a birnin Bukoba a gabar tafkin Victoria.
'Yansanda sun bada rahoton cewa kimanin mutane 100 sun jikkata kuma ana ci gaba da ayyukan ceto a lardin kagera.
Hukumar kula da harkokin karkashin kasa ta Amurka tace an ci girtgizar kasashe makwabta kamar Rwanda da Burundi, da Ugand a da kuma kenya.
Sanarwa daga ofishin shugaban kasar ta bayyana bakin cikin da jimamin hasarar rayuka da dukiya da aka yi, sai dai bata bada wani karin bayani ba.
Girgizar kasa ba wani sabon abu bane a yankin na Great lakes, sai dai basu da karfi ainun.
Ahalinda ake ciki kuma, shugaban kasar kenya ya ayyana wata sabuwar jam'iyyar siyasa da ake kira Jubilee, jam'iyar da yake shirin takara karkashinta domin wa'adi na biyu kuma na karshe a zaben kasar kasar da za'a yi badi.