A cikin hudubarsa limamin yayi fatan yafewa da kuma tausayawa juna tsakanin Musulmi.
Ministan yada al'adun Nijar Asumana Malam Isah yace kiran da limamin yayi na nufin kowa ya san ranar layya rana ce ta tausayawa marasa karfi, a kama masu. Yakamata a ce yanka da aka yi wanda bai yi ba shi za'a ba domin a taimaka masa. Yin hakan yana cikin jinkai.
Hadin kan 'yan siyasa domin a sa kai a bautawa kasa na cikin yafewa juna. Yakamata a ce abubuwan cigaba da samun zaman lafiya an samesu tare da juna.
Shekaru biyu ke nan da yankin Diffa yake fama da matsalar tsaro. Saboda haka ne ministan tsaron cikin gida Bazu Muhammad yayi anfani da damar ya kira Musulmi su cigaba da taimakawa kasar da addu'ar Allah Ya tabbatar da zaman lafiya a kasar da kwanciyar hankali da kawo saukin yanayin tsaro.
Ministan ya kira jama'a da su sa ido kan duk wani da basu yadda dashi ba su shaidawa jami'an tsaro domin hana aukuwar ta'adanci.
Dangane da halin da jama'a suka yi sallah a birnin Yammai, mazauna birnin sun tabbatar lami lafiya suka yi sallah.
Ga rahoton Yusuf Abdullahi da karin bayani.