Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Zabe a Malawi ta Ayyana Dan Hamayya Peter Mutharika a Matsayin Wanda Ya Lashe Zaben Shugaban Kasar


Hoton Peter Mutharika, wanda ya lashe zaben shugaban kasar Malawi, da aka gudanar ranar talata.
Hoton Peter Mutharika, wanda ya lashe zaben shugaban kasar Malawi, da aka gudanar ranar talata.

A daren Jumma'a ne hukumar ta bayyana sakamakon zaben kasar da aka yi ranar talata, amma da gardandami.

A Malawi, jami’an hukumar zaben kasar sun ayyana shugaban ‘yan hamayya Peter Mutahrika, a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi makon jiya, wanda kuma ya janyo gardama.

A daren jumma’a ne hukumar zaben ta bayyana sakamakon zaben a Blantyre cibiyar kasuwancin kasar, sa’o’I bayanda masu zaganga zanga da suke neman a sake kidaya kuri’un da aka kada a zaben, suka kara da ‘Yansanda a birnin Mangochi, dake kudancin kasar. Mutum daya ya rasa ransa sakamakon tarzomar.

Sakamakon karshe da hukumar ta bayar ya nuna Mr. Mutahrika na jam’iyyar DPP ya sami nasara da kashi 36 cikin dari na kuri’u da aka kada, yayinda dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar MCP Lazrous Chakawa, ya sami kashi 29 cikin dari.

Shugabar kasa mai ci Joyce Banda, tazo ta uku da kashi 20 cikin dari. A wani lokaci yau Asabar ake sa ran za a a rantsar da Mr. Mutharika, wanda dan uwan shugaban kasar mai rasuwa Bingu wa Mutahrika ne.

A wani gefen kuma, jami’an MDD sun ce fiyeda ‘yan tawaye dari ne na kungiyar ‘yan tawayen Hutu daga kasar Rwanda, suka mika makamansu a wani biki da aka shirya na musamman a gabashin jamhuriyar demokuradiyyar kwango.
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG