Dama kafin shigar da wannan bukata,’yan majalisar dokokin na masu rinjaye na zargi shugaban majalisar dokokin Nijer ne da hanna ruwa kudu akan alalmuran da suka shafi jagorancin tafiyar da majalisar.
‘Yan majalisar,masu rinjaye sun ce tabi’un shugaban majalisar ya samo asalin ne tun lokacin da ya rikida ya kuma dan adawa.
Zakari Umaru,dan majalisar dokokin PNDS taraiya ne mai mulki yace “mu a ganin mu bai dace ba Hama Amadu ya ci gaba da jagarancin majalisa,laifinshi ya tauye aikin majalisa, ya hana ayi shi, kuma ga shaida iri-iri mun kai inda zamu tsaya muce majalisa bata da shugaba.
Bangaren masu adawa suma sun kira taron manema labarai domin maida martini kan sabuwar bukatar dasu masu rinjaye suka shigar a gaban kotu koli ta tsarin mulki.
Saleh Hassan Amadu dan majalisar dokokin jamiyar Lumana Afirka.ta Hama Amadu,yace “yau gashi nan sun ce su gobe in Allah ya kaimu zasu tsige shugaban majalisa,kennan dimokradiya ya mutu a Nijer har abada.
Tsawon kwanaki sama da goma sha biyar kennan da wani rashin jituwa ya barke a majalisar dokokin jamhuriyar Nijer tsakanin yan adawa da masu rinjaye kan batun nada mukamai biyu na koli na tafiyar da majalisa dokokin.
Wannan sabon matakin da masu rinjaye suka dauka wasu na ganin sa tabkar wani sabon salo da masu rinjaye suka bullo dashi domin cimma bukatarsu ta tsige shugaban majalisar dokokin Nijer,mutun na biyu mafi kima a jerin mahukumtar Nijer, amma kuma dan adawa.