A Djibouti jami’an kasar suka ce wasu fashe fashe biyu sun kashe akalla mutane biyu a wani zauren cin abinci da baki daga kasashen yammacin duniya suke yawaita zuwa.
Hukumomin kasar suka ce akalla wasu mutane 10 sun jikkata a fashe fashen d asuka auku a daren jiya Asabar a maciyar abincin da ake kira La Chaumiere dake a tsakiyar babban binrin kasar.
Babu wanda ya fito nan da nan ya dauki alhakin kai harin.
Djibouti dake can kuriyar Afirka Faransa ce tayi mata mulkin mallaka, kuma akwai sansanonin sojin Faransa da Amurka a kasar.
Kasar ta tura sojojinta cikin runduar sojojin kiyaye zaman lafiya na kungiyar hada kan kasashen Afirka da take fafatawa da kungiyar al-shabab a Somalia.