Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kai Harin Bama-Bamai a Kenya; Mutane Akalla 10 Sun Mutu.


Hayaki yake tashi bayanda jami'an tsaro suka tarwatsa bam a kenya.
Hayaki yake tashi bayanda jami'an tsaro suka tarwatsa bam a kenya.
A Kenya wasu tagwayen bama-bamai sun tashi cikin wata kasuwa da take cike da mutane kusa da birnin Nairbi, akalla mutane 10 sun mutu, wasu 70 kuma sun jikkata.

‘Yansanda suka ce an tada nakiyoyin biyu shigen irin waddanda aka hada a gida jiya jumma’a, a cikin kasuwar da take kusa da tsakiyar birnin Nairobi fadar kasar. Suka ce daya daga cikin bama-baman ya afkawa wata motar fasinja.

Fefen vidiyon inda aka kai harin ya nuna motoci da suka lalace da baraguzai da tagogin gilashi da suka farfashe cikin ginin.

Nan da nan dai babu wanda ya fito ya dauki alhakin kai harin, sai dai babban baturen ‘Yansandan birnin Nairobi Benson kibui yace an tsrae mutane biyu domin a yi musu tambayoyi.

A farkon makon nan Amurka da Britaniya sun fidda sanarwa ga ‘ya’yan kasashen biyu cewa su yi takatsan-tsan na yin balaguro zuwa Kenya saboda akwai yiyuwar akai hari.
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG