Bai wa jama’ar damar samun dukkan wasu bayanan da suke bukata kai tsaye game da yaki da cin hanci a Jamhuriyar Nijer ya sa hukumar yaki da cin hanci HALCIA bude shafin yanar gizo mai adireshin WWW.HALCIA.NE matakin dake zama wata hanyar nuna alamar gudanar da abubuwa a fili, inji mataimakin shugaban wannan hukuma, Alhaji Salissu Ubandoma.
Samun bayanai daga jama’a akan wani abin da suke zargin gano alamun cin hanci wajen gudanar da shi wata babbar gudunmuwa ce da ake ganin za ta taimaka wajen rage kaifin cin hanci a wannan kasa, mafari kenan da hukumar ta HALCIA ta bude shafukan kafafen sada zumunta irinsu facebook da tweeter da Youtube da dai sauransu, inji shugabanta mai shari’a Abdurrahman Ghousman.
Shugaban kungiyar yaki da cin hanci ta ANLC reshen transparency a Nijer, Malan Maman Wada ya yaba da wannan yunkuri, koda yake a ra’ayinsa samar da layin waya ne ya fi dacewa da wannan bukata ganin yadda akasarin ‘yan Nijar ba su yi ilimin boko ba.
A rahoton da ta fitar a makon jiya hukumar yaki da cin hanci ta sanar cewa ta fara samun nasarori a yakin da ta kaddamar, inda dubun wasu masu kewaye hanyoyin biyan haraji da kudaden awon kaya ta cika kamar yadda asirin ya tonu a wajen masu satar jarabawa da masu kamfanin damfara inji hukumar ta HALCIA.
Wakilinmu a birnin Yamai Souley Moumouni Barma ya aiko mana karin bayani:
Facebook Forum