A jamhuriyar Nijer zagayen da dan takarar jam’iyar PNDS Tarayya, Bazoum Mohamed, ya gudanar a wasu yankunan kasar ya janyo suka daga bangaren ‘yan adawa wadanda ke zargin jam’iyar mai mulki da soma yakin neman zabe, har ma shugabaninta na amfani da kadarorin gwamnati wajen neman yardar talakawa sabanin abubuwan da dokoki su ka yi tanadi.
Wannan shine zagaye mafi girma da shugaban jam’iyar PNDS Tarayya ke gudanarwa a yankunan karkara tun bayan da aka tsayar da shi a matsayin dan takarar shugaban kasa na shekarar 2021 mai zuwa a watan maris din da ya gabata.
Bayan yankunan Dosso da Tahoua tawagar ta Bazoum ta ziyarci yankin Zinder, la’akari da faruwar wasu abubuwan a yayin jerin gangamin da jam’iyar mai mulki ta gudanar ya sa ‘yan adawa zargin an taka doka.
Garba Hambali Dauda shine sakataren jam’iyar adawa ta MPN Kishin kasa, yace kamfen ne ya je yi bawai yaje ganin yan kasa ba, kuma take taken da ake yi na nunu da cewa ba za’a yi adalci ba a binciken da ake yi.
Sai dai Bazoum Mohamed na cewa akwai rashin fahimtar nauyin da ya rataya a wuyan dan siyasar da ke fatan samun karbuwa a wurin talakawa.
Hotunan da aka yada a shafukan sada zumunta sun yi nuni da cewa dan takarar na PNDS Tarayya ya yi amfani da motarsa ta ministan cikin gida a yayin wannan zagaye to amma a cewarsa shi da kansa yasan cewa anan ya aikata ba dai dai ba.
Ana su bangare ‘yan adawa na ganin ya kamata doka ta yi aikinta don kawo karshen aikata irin wannan mumunar dabi’a ta ‘yan siyasa anan gaba.
Tsarin jadawalin da hukumar zabe ta fitar a karshen makon jiya na cewa a ranar 27 ga watan Disambar 2020 ne za a gudanar da zagayen farko na zaben shugaban kasa, a yadda jam’iyun siyasa ke gwagwarmayar neman yardar talakawa a yayin da ya rage sama da shekara 1 a halarci runfunan zabe, alamu na nuni da cewa za’a kece raini sosai a tsakanin ‘yan takarar da ke fatan dare kujerar shugabancin kasa.
Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma daga Yamai:
Facebook Forum