Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyin Mayaka A Kongo Da Uganda Na Fakewa Da ISIS


Wasu jami'an tsaro
Wasu jami'an tsaro

Kwararru na gargadin cewa mayar da hankalin da ake yi kan ko mene ne tushen wata kungiya mai tsattsauran ra’ayin addini, na gurgunta matakan da ake daukawa kan ‘yan tawayen a Mozambique da Janhuriyar Dimokaradiyyar Congo.

Wasu kungiyoyin tawaye a yankunan na ikirarin alaka da kungiyar ISIS don su ruruta karfinsu, alhalin ko babu abin da ya hada su da ISIS, a cewar wasu kwararru a yankin.

Wani harin da aka kai ranar 18 ga watan Afrilu kan wani sansanin soji daura da kan iyakar Congo da Uganda, ya yi sanadin mutuwar sojojin Congo da dama, baya ga wadanda su ka ji raunuka.

Shi ne harin farko da aka alakanta da kungiyar Wilayat ta Yankin Tsakiyar Afurka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG