Hukumar lafiya ta Duniya WHO, ta ce cutar Ebola mai saurin kisa, na ci gaba da yaduwa a wasu sabbin yankuna da ke gabashin Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, yayin da adadin wadanda suka kamu da cutar ya doshi 3,000.
Adadin baya-bayan nan, ya nuna cewa mutum 2,934 ne suka kamu da cutar, inda 1,965 daga cikin wannan adadin, suka rasa rayukansu.
Babban Darekta a hukumar ta WHO, Michael Ryan, ya yi gargadin cewa, akwai yiwuwar cutar ta ci gaba da yaduwa, saboda wasu dalilai.
“Zantukan da ake ta yamadidi da su cewa, ana amfani da allurar rigakafin cutar, wajen yada ta, da kuma karasa masu dauke da ita, da kungiyoyin da ke watsa bayanai marasa tushe ta kafofin sada zumunta, na kawo cikas a yakin da ake yi da cutar.”