Hukumar alhazan Najeriya NAHCON, ta ce za ta binciki dalilin da ya sanya wasu alhazan jirgin yawo suka gudanar da zanga-zanga a filin saukar jiragen sama na Malam Aminu Kano don rashin jigilarsu zuwa Saudiyya.
Wata sanarwa da jami’ar yada labarai a hukumar alhazan Najeriyar, Fatima Sanda Usara, ta nuna cewa, hukumar ba ta samu wani korafi na kalubale daga duk kamfanonin da suka yi wa rijista na alhazan jirgin yawo ba, har aka kammala jigilar alhazan.
Bisa faruwar wannan lamarin, NAHCON ta bukaci wadanda lamarin ya shafa su rubuto korafi da takardun da za su nuna irin yanayin hidima da su ka biya ta kujerar hajjin don a samu a gudanar da bincike a bi musu hakkinsu.
A wani labari na daban kuma kan aikin hajjin, shugaban hukumar alhazan Najeriya, Barista Abdullahi Mukhtar, ya ce za a bullo da wata shaida ga alhazan musamman don rage cunkoso a tantunan Muna daga 'yan alfarma.
Wannan ya biyo bayan labarin korafin wasu alhazai.
Tuni dai aka fara jigilar dawo da alhazan Najeriya gida bayan kammala aikin hajjin na bana.
Saurari cikakken rahoton Saleh Shehu Ashaka daga Makkah:
Facebook Forum