Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Lafiya Ta Duniya Ta ce Za Ta Taimaka Wa Najeriya Wajen Tabbatar Da Tsabtataccen Muhalli


Hukumar Lafiya Ta Duniya Za Ta Taimakawa Najeriya Wajen Tabbatar Da Tsabtataccen Muhalli
Hukumar Lafiya Ta Duniya Za Ta Taimakawa Najeriya Wajen Tabbatar Da Tsabtataccen Muhalli

Hukumar lafiya ta duniya na yunkurin taimaka wa Najeriya wajen tabbatar da kula da lafiyar muhalli wanda ake sa ran zai taimaka wajen kare lafiyar al'umma.

SOKOTO, NIGERIA - Hukumar lafiyar ta sauya tunaninta zuwa kula da muhalli ne saboda ganin ta jima tana kokarin inganta lafiyar jama'a amma kuma bai hana barkewar curutuka ba, wadanda wasu lokuta kan yi sanadin salwantar rayukan jama'a da dama.

Hukumomin da ke bayar da tallafi na kasashen duniya kamar Hukumar Lafiya ta Duniya da Asusun Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya da makamantansu, sun jima suna kashe makudan kudi wajen inganta rayukan ‘yan Najeriya, sai dai har yanzu kwalliya ta kasa biyan kudin sabulu yadda ake muradi, domin har yanzu ana samun barkewar cututtuka kamar kwalara da makantanta a Jihohin Najeriya, abin da ya tilasta wasu daga cikin hukumomin bayar da tallafi sauya tunani.

Darakta a Ma'aikatar Kare Muhalli ta Jihar Sakkwato, Aminu Liman, ya ce Hukumar Lafiya ta Duniya ta zabi jihohi shida a Najeriya domin ganin yadda za ta bayar da tallafi a haujin kula da lafiya da tsaftar muhalli ko da hakan zai taimaka wajen rage barkewar cututtuka masu kashe jama'a.

A binciken da hukumar lafiya ta duniya ta jagoranci gudanarwa a wasu Jihohin Najeriya, an gano matsalolin da ke gurbata muhalli har a kai ga samun barkewar cututtuka da suka hada da, yin bahaya a fili, rashin tsarin makewayi mai tsafta da yadda ake amfani da kashi a matsayin taki a gonaki, da rashin isassun ruwan kula da tsaftar jiki da ta muhalli.

Hukumar Lafiya Ta Duniya Za Ta Taimakawa Najeriya Wajen Tabbatar Da Tsabtataccen Muhalli
Hukumar Lafiya Ta Duniya Za Ta Taimakawa Najeriya Wajen Tabbatar Da Tsabtataccen Muhalli

Jami'in tuntuba na hukumar lafiya ta duniya, Dokta Aminu Sa'idu Madaki, ya ce hukumar lafiyar tana son ilimantar da jihohin Najeriya ne kan yadda za a kare muhalli don kauce wa bullar cututtuka. Ya ce dole sai gwamnati ta dauki matakai ciki har da samar da isassun ruwa ga jama'a na kula da tsaftar jiki da muhalli.

Har ila yau wasu ‘yan kasa na ganin ko bayan daukar matakan magance wadannan matsalolin, akwai bukatar gwamnatoci su kula da tsarin gine-gine a cikin garuruwa ta yadda za a kauce wa cunkoson jama'a wuri daya.

Uban kasar Gagi a jihar Sakkwato, Sani Umar Jabbi, wanda ke cikin masu irin wannan ra'ayi ya ce ya kamata a kula da magance yadda ake samun cunkoso cikin gidajen jama'a saboda rashin bin tsarin zamani a yayin gine-ginen gidaje.

A jihar Sakkwato da ke arewa maso yammacin Najeriya hukumomin jihar sun hadu da jami'an hukumar lafiya ta duniya domin tantance rahoton binciken da aka gudanar da zummar aiki da shi ko za a samu kwalliya ta biya kudin sabulu a wannan haujin.

Babban Sakatare a Ma’aikatar Kare Muhalli, Mu'azu Abubakar Madawakin Sakkwato, ya ce gwamnati za ta kara azama wajen ganin anyi aiki da shawarwarin da aka bayar don kare muhalli da lafiyar al'umma baki daya.

Yanzu haka hukumar lafiya ta duniya na gudanar da wannan aikin a jihohi shida na Najeriya, idan aka samu biyan bukata akwai yuwuwar ya game dukan jihohin kasar domin Kare lafiyar jama'ar kasar.

Saurari cikakken rahoto daga Muhammadu Nasir:

Hukumar Lafiya Ta Duniya Za Ta Taimakawa Najeriya Wajen Tabbatar Da Tsabtataccen Muhalli.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:18 0:00

XS
SM
MD
LG