Wannan shari’a dai jaddada hukunci ne da babbar kotun tarayya ta jihar Legas ta yanke, da shima ya baiwa hukumar ta gwamnatin Najeriya hurumin kula da lamuran tattalin arziki na bakin teku.
Abu Zakariyya, dake zama lauya mai zaman kansa, ya ce kungiyar ‘yan fito na da hurumin ‘daukaka kara zuwa kotun koli. Yana mai jaddada cewa dokar gwamnatin Najeriya ce ta kafa hukumar sufurin jiragen ruwa da ake kira ‘Shippers Council’ don haka ne ‘yan fito basu samu nasara ba a manyan kotuna biyu na baya.
A cewar Ibrahim Mohmmad Kashim, mai bayar da shawara ga kamfanoni ta hanyar da zasu sami riba, ya ce a wani taro da suka yi a Legas da kwararru na fannin hada-hadar kasuwancin jiragen ruwa, inda kowa ke cewa idan har gwamnati ta baiwa hukumar sufurin jiragen ruwa goyon bayan da ya cancanta, tabbas kudaden shigar da gwamnati zata samu zai wuce abin da take samu a fannin Man Fetur.
Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.
Facebook Forum