Gwamnoni da sarakunan gargajiya a jihohin yankin arewacin Najeriya sun nuna goyon bayansu ga tsarin kafa rundunar ‘yan sanda a matakin jiha, a wani yunkuri na magance matsalolin tsaro da yankin ke fama da su.
Yayin wani taro da suka gudanar a Abuja a ranar Talata, gwamnonin da sarakuna sun amince da tsarin wanda suka ce zai taimaka wajen shawo kan matsalolin tsaro a daukacin kasar.
An kwashe shekaru da dama ana kai ruwa rana dangane da kafa rundunar ‘yan sanda a matakin jihohi, lamarin da ya yi ta haifar da muhawara.
A baya, Majalisar dokokin Najeriya ta ki amincewa da wannan tsari saboda ana gudun kada gwamnonin su rika wuce gona da irin, wajen amfani da ‘yan sandan don muzgunawa ‘yan adawa.
Sai dai a sanarwar karshen taro da suka fitar a otel din Transcorp Hilton da ke Abuja, gwamnonin da sarakunan gargajiyar sun yanke shawarar nuna goyon baya a sauya kundin tsarin mulkin kasar, don a samar da gurbin kafa rundunar ‘yan sandan jiha.