Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kudu Ce Za Ta Karbi Shugabanci A 2023 - Gwamnonin Kudu


Wasu daga cikin gwamnonin jihohin kudancin Najeriya (Twitter/ Seyi Makinde)
Wasu daga cikin gwamnonin jihohin kudancin Najeriya (Twitter/ Seyi Makinde)

Kazalika gwamnonin sun kara jaddada matsayarsu ta cewa Najeriya ta ci gaba da zama a matsayin kasa dunkulalliya bisa tsari na adalci.

Gwamnonin kudancin Najeriya 17, sun cimma matsaya daya kan amincewa da mulkin karba-karba tsakanin kudu da arewa kasar, inda suka ce, su za su fitar da dan takarar shugaban kasa a zaben 2023.

Kungiyar gwamnonin ta kai ga cimma wannan matsaya ce, yayin wani taro da ta gudanar a jihar Legas a ranar Litinin.

“Kungiyar ta amince a mataki na bai daya cewa, a rika mulkin karba-karba tsakanin kudanci da arewacin Najeriya. Ta kuma amince cewa, shugaban Najeriya na gaba, ya fito daga yankin kudanci.” In ji sanarwar da kungiyar ta fitar a karshen taron wacce ke dauke da sa hannun shugaban kungiyar, gwamnan jihar Ondo, Arakunrin Oluwarotimi Odunayo Akeredolu.

Kazalika gwamnonin sun kara jaddada matsayarsu ta cewa Najeriya ta ci gaba da zama a matsayin kasa dunkulalliya bisa tsari na adalci.

Ga wasu daga cikin sauran batutuwan da taron gwamnonin kudancin na Najeriya ya cimma matsaya a kai:

- Taron ya yabawa jami’an tsaro kan namijin kokarin da suke yi wajen tabbatar da zaman lafiya tare da jajintawa iyalan jami’an tsaron kasar da suka rasa ‘yan uwansu.

- Jaddada bukatar a samar da ‘yan sandan jiha

- Taron ya amincewa a duk lokacin da jami’an tsaro za su kai wani samame a kowacce jiha, dole a rika sanar da babban mai tsaron jihar (gwamna)

- Taron bai lamunta da yadda ake nuna son kai wajen aiwatar da hukunci ba sannan ya nuna cewa a duk lokacin da za a kama wanda ake zargi da laifi, a yi hakan bisa tsarin doka da tabbatar da ‘yancin bil adama.

- Taron gwamnonin har ila yau, ya amince cewa ranar Laraba 1 ga watan Satumba, 2021 dokar haramta kiwo a fili za ta fara aiki a duk jihohin yankin kudancin kasar.

- Gwamnonin yankin ba su amince da kaso 3 da za a rika ba jihohin da ake tono arzikin mai ba, amma suna goyon bayan kashi 5 kamar yadda majalisar wakilai ta ba da shawara.

XS
SM
MD
LG