Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Neman Turawan da Aka Sace a Kamaru


​A halin da ake ciki batun sace wasu Italiyawa biyu da wata ‘yar Kanada daya, a kasar Kamaru, yanzu an baza sojoji, da jiragen masu saukar ungulu, da sojoji a kasa, da kuma babura suna zagaye ko zasu gano su.

A wani labari da aka samu a baya-bayannan, alamu na nuna cewa ba’a fitar da mutanen daga kasar Kamaru ba, saboda iyakokin kasar a rufe suke.

Gwamnatin Kamaru itace take daukar nauyin dawainiyar neman wadannan jami’ai, gabannin kaddamar da bunkasar sojojin kasar.

A halin yanzu dai, bincike ya tsananta saboda wannan lamari ya daure wa jama’a kai saboda an sace wadannan mutanen ketare ne, a kusa da shedkwatar jihar.

Ranar Juma’ar nan da ta wuce ne, misalign karfe 12 na dare, wasu mutane masu yawa akan babura dauke a garin Jere, dauke da makamai. Anan ne suka dauke mutanen mabiya addinin Kirista, da kuma mota kirar Suzuki.

Italiyawan sun hada da Giampaolo Marta mai shekaru 47 da haihuwa, da kuma Gianantonio Allegri mai shekaru 57 da haihuwa.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:45 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG