Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Aikin Shara Sun Yi Zanga Zanga


Masu zanga-zanga
Masu zanga-zanga

Matasan dai sun ce an yaudaresu sun zabi Gwamnati amma an yi watsi dasu

Gwamnatin jahar Bauchi ta sallami daruruwan matasa dake yiwa Gwamnatin jahar aikin sharan tituna abunda ya jawo bacin rai ga matasan.

Daruruwan matasa sun gudanar da zanga zanga a kofar filin wasa na Abubakar Tafawa Balewa, domin nuna rashin jindadinsu dagane da korar su daga aiki da kuma kasa biyan su albashin su na tsawon watani biyar.

Matasan dai sun ce an yaudaresu sun zabi Gwamnati amma an yi watsi dasu tunda an kore su daga aiki da kuma kasa biyan su kudaden albashi na watani.

Wakilin muryar Amurka ya bi tuntubi hukumar da abun ya shafa inda mai rike da mikamin babban sakatare Shehu Aliyu Darazau, ya ce game da korafin ma’aikatan an kafa wani kwamiti kuma yana nazarin biyan su kudaden su.

Ya kuma kara da cewar Gwamnati na duba yuwar maido da wasu daga cikin su wanda za’a gudanar kadan da kadan.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:57 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG