'Yan sari-ka-noken kungiyar Hezbollah ta Lebanon, sun ce zasu ci gaba da kai hari kan sojojin Isra'ila a yankin gonakin Shebaa da ake rikicinsu a bakin iyakar Lebanon da Isra'ila.
Waata sanarwar da kungiyar ta bayar ta ce ba zasu mika wuya ga matsin lambar sakataren harkokin wajen Amurka, Colin Powell, ba.
Sakatare Powell ya ziyarci Lebanon da Sham(Syria) a jiya litinin, inda ya roki gwamnatocin kasashen da su hana Hezbollah kai hare-hare kan Isra'ila. Kasashen Sham da Farisa(Iran) sune manyan masu goyon bayan kungiyar ta Hezbollah, wadda ta lashi takobin sai ta fatattaki Isra'ila daga gonakin na Shebaa.
Hezbollah ta kaddamar da kai hare-hare kusan kullum a bayan da Isra'ila ta kaddamar da farmakinta a yankin Yammacin kogin Jordan ranar 29 ga watan Maris. Isra'ila ta maida martani ta hanyar luguden wuta da bindigogin igwa tare da kai hare-hare ta sama zuwa kudancin Lebanon, abinda ya haddasa fargabar cewa rikici na iya bazuwa a fadin Gabas ta Tsakiya.