An samu hadarin kwale kwalen ne a garin Ginga na karamar hukumar Shagari a jihar Sakkwato wanda ya hallaka mutanen 13.
Tuni dai aka yi jana'izar mutanen kuma jama'a na ci gaba da yin ta'aziya ga iyalan.
Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya yi, shi ma tsohon gwamnan Sakkwato kuma shugaban kwamitin tsaro a majalisar dattawa , Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko na cikin daruruwan jama'ar da suka yi ta'aziya ga iyalan.
Bisa ga lura da yadda hatsarin kwale-kwale ke lakume rayukan jama'a, masana sun jima suna baiwa gwamnatoci shawarwari na yadda za'a iya shawo kan wannan matsalar.
Farfesa Bello Baudan ya bayar da shawara cewa hukuma ya kamata ta tanadi jiragen masu kyau da jama’a za su yi amfani da su don tsallake Kogi, saboda a kula da lafiyar mutane.
Kuma ya ce dole ne a tabbatar da cewa ba a masu lodi ya wuce ka’ida saboda nauyi da kifewa, da kuma tabbatar da lafiyar ruwan.
Wata kila idan aka mayar da hankali ga wadannan shawarwarin a samu saukin irin wadannan matsalolin.
Saurari rahoto cikin sauti daga Muhammadu Nasir: