Dakarun Najeriya, sun ce sun halaka mayakan kungiyar ISWAP akalla 50 tare da hadin gwiwar dakarun saman kasar da ke aiki karkashin shirin “Operation Hadin Kai.”
Lamarin ya faru ne a ranar Laraba a cewar wata sanarwa da kakakin rundunar sojin kasar Birgediya Janar Mohammed Yerima ya fitar, yayin da mayakan kungiyar suka kai wani hari karamar hukumar Damboa da ke jihar Borno.
A cewar sanarwar, mayakan sun sha kai hari akan garin Damboa da muggan makamai da suka hada da motocin masu dauke bindigogi da na kakkabo jiragen sama.
“Amma dakarunmu sun yi nasarar kassara su, inda suka lalata motocin, sannan suka kashe 50 daga cikinsu, lamarin da ya tilastawa sauran da suka tsira arcewa.” In ji Yerima.
Sojojin Najeriyar sun ce sun kuma kwato makamai da dama daga hannun mayakan.
Karin bayani akan: Manjo Janar Faruk Yahaya, ISWAP, Boko Haram, jihar Borno, Nigeria, da Najeriya.
Sabon babban hafsan sojin kasa, Manjo Janar Faruk Yahaya, ya jinjinawa dakarun saboda wannan nasara da suka samu.
Yankin jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, ya kwashe sama da shekara 10 yana fama da hare-haren kungiyar Boko Haram da kuma ISWAP da ta bangaren daga jikin Boko Haram.
Dubban mutane sun mutu sanadiyyar hakan, sannan wasu miliyoyi sun rasa muhallansu.