Wannan kuwa yana zuwa lokacin da jama'a ke ci gaba da jimamin abinda ya faru na hadarin kwale kwalen.
Daga ranar da hadarin ya faru zuwa yanzu an samu lalabo gawarwakin mutane 97 kuma tuni al'amurra sun koma yadda suke a garin na Warrah sai dai wadanda suka rasa ‘yan uwa har yanzu suna jimamin rashin duk da yake sun soma samun tallafi.
Tallafin an bayar da shi ne daga cikin kudaden da aka tara a matakin karamar hukumar wadanda masu zuwa ta'aziya suka bayar a cewar shugaban karamar hukumar Ngaski Abdullahi Buhari Warrah.
Ita kuwa gwamnatin jihar Kebbi taro ta yi na majalisar zartaswa na musamman na bita da juyayi tare da nuna gamsuwa ga wadanda suka jajantawa gwamnatin akan wannan ibtila'in.
Shugaban hukumar bayar da agajin gaugawa Sani Dododo wanda ya yau wa manema labarai bayani ya ce an dauki matakai na binciken dalilin wannan matsalar da kuma kaucewa sake faruwar irin ta.
Duba da cewa wadanda suka rasa iyayensu a wannan ibtila'in na iya kasancewa cikin wani hali duk da tallafin da suka soma samu, ina aka kwana da tallafin da gwamnatin jihar ta Kebbi wanda ya haura naira miliyan dari da Kari?
Baya ga mutum 22 da suka tsira da kuma gawarwakin mutum 97 da aka samu akwai yiwuwar wasu gawarwaki sun bi ruwa ko kuma suna kasan buraguzzan jirgin da ya nutse wanda mahukunta ke fatan lalabowa a karshen wannan mako.
Saurari cikakken rahoton a cikin sauti: