Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kusoshin Jam’iyar Democrat Sun Goyi Bayan Janyewar Biden Daga Sake Takarar Shugaban Kasa


Shugaba Joe Biden
Shugaba Joe Biden

Kusoshin jam’iyar Democrats da su ka hada da tsohon Shugaban kasa Barak Obama, da tsohuwar Kakakin Majalisar Wakilan Amurka Nancy Pelosi sun yabi Shugaban kasa Joe Biden domin janyewa daga takarar Shugaban kasa a zaben da za a gudanar a watan Nuwamba

Jim kadan bayan sanar da janyewa daga takara da kuma nuna goyon bayan mataimakiyar Shugaban kasa Kamala Harris a matsayin wadda za ta maye gurbinshi a takarar, ‘yan jam’yar Democrat da dama da suka hada da ‘yan majalisa, gwamnoni, da sauran jiga-jigan jam’iyar masu ikon fada a ji, suka nuna goyon bayan matakin , yayinda wadansu kuma suka fara goyon bayan neman tsayar da Kamala Harris a shafukansu na sada zumunta.

Tsohon Shugaban kasa Barak Obama ya fitar da sanarwa inda ya bayyana goyon bayan shawarar da Biden ya yanke na janyewa daga takarar. Ya ce "Yana ganin damar da ke gabanshi a fagen siyasa, ya yanke shawarar mika tikitin takarar ga wani daban, babu shakka wannan yana daya daga cikin mawuyatan matakan da ya dauka a rayuwarsa. Amma na san shi, ba zai yanke wannan shawarar ba sai dai idan ya yi imanin cewa, wannan ne mafi alheri ga Amurka."

Obama ya kuma ce, "Za mu shiga wani sabon babi a cikin kwanaki masu zuwa. Amma ina da kwarin gwiwa cewa, Shugabannin jam'iyyarmu za su iya samar da tsarin da za a tsayar da fitaccen dan takara."

Tsohuwar Kakakin Majalisar Wakilan Amurka Nancy Pelosi ta wallafa cewa, "Shugaba Joe Biden Ba'amurke ne mai kishin kasa wanda a ko da yaushe ya ke sa kasarmu a gaba. Abubuwan da ya gada na hangen nesa, dabi'u, da jagoranci sun sanya shi ya zama daya daga cikin shugabannin da suka fi dacewa a tarihin Amurka. Amurka tana baiwa mutane damar cimma gurinsu, Allah ya albarkaci Amurka, da girman Joe Biden, da kuma kirkin shi.

Tsohon Shugaban kasa Bill Clinton da maidakinsa Hillary sun fitar da sanarwar hadin guiwa inda suka jinjinawa Shugaba Biden domin janyewa daga takarar, suka kuma bayyana goyon bayan Kamala Harris.

Sun ace, "Muna da farin cikin shiga cikin Shugaban kasa wajen amincewa da Mataimakiyar Shugaba Harris kuma za mu yi duk abinda za mu iya don tallafa mata."

Shima tsohon dan takarar Shugaban kasa Bernie Sander dan Majalisar dattijai da baya takara karkashin tutar wata jam’iya, daya daga cikin wadanda suka nemi Biden kada ya janye daga takarar, ya nuna goyon bayan takarar Kamala Harris "Joe Biden ya bauta wa kasarmu da daraja. A matsayinsa na shugaban kasa na farko da ya taba fita ya mara wa ma'aikata masu yajin aiki baya, ya kasance Shugaban kasan da yafi nuna kishi da kyautatawa ma’aikata a tarihin Amurka a zamanin nan. Na gode Shugaban kasa da duk abinda ka yi."

Sauran fitattun ‘yan jam’iyar Democrat da suka bayyana bayan tsaida Kamala Harris a matsayin ‘yar takarar jam’iyar Democrat sun hada da daya daga cikin wadanda suka nemi takarar shugabancin Amurka Elizabeth Warren, wadda ita ma kamar Sanders, ta nuna goyon bayan Biden ya ci gaba da takara ta rubuta cewa, "Shugabancin Joe Biden ya kawo canji. Ya yi aiki tukuru a cikin shekaru hudun da suka gabata - don dawo da ayyukan yi, tsayawa tsayin daka ga manyan kamfanoni, da gina tattalin arziki wanda zai iya haifar da ci gaba da ya amfane mu duka, fiye da yadda muka iya yi a cikin shekaru arba'in da su ka shige, ya cancanci yabo don samun nasarar doke Donald Trump a 2020.”

Duk da yake babu tabbacin jam’iyar Democrat zata tsayar da Kamala Harris a matsayin ‘yar takarar jam’iyar, kungiyoyi da daidaikun jama’a sun bi sahun Shugaba Biden wajen nuna goyon bayan tsaida mataimakiyar Shugaban kasar a matsayin ‘yar takarar jam'iyar.

Kungiyar ‘yan Majalisar dokokin Amurka bakaken fata ta fitar da sarnawa inda ta ce tana da kwarin guiwa cewa, Kamala Harris zata yi jagorancin kwarai. A cikin sanarwar da ta firar, kungiyar ta ce, “Ta taka rawar gani a nasarorin da aka samu a cikin shekaru 3.5 da suka gabata, kuma ta bada gagarumar gudummuwa wajen rage yawan mace-macen mata masu juna biyu, da kare ‘yancin haihuwa, da kuma tabbatar da damar samun inganci a fannin tattalin arziki ga kowa. Za ta yi kyakkyawan aiki a matsayin Shugabar Amurka."

Wannan ne karon farko da wani Shugaban kasa ya janye daga takara watanni kalilan kafin babban zabe, lamarin da ya sa ya zama wajibi jam'iyar Democrat daukar matakin gaggawa domin tsaida wanda zai yi mata takara da ya yiwu ya hada da zaben mataimaki idan jam'iyar ta amince da tsaida Kamala Harris a matsayin 'yar takara.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG