Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abin Da Kwararru Ke Cewa Kan Janyewar Biden Daga Takarar Shugaban Kasa


Shugaban Amurka Joe Biden a dakin Roosevelt na Fardar White House, Washington
Shugaban Amurka Joe Biden a dakin Roosevelt na Fardar White House, Washington

Kwararru a fannin siyasa da gudanar da mulki a Najeriya sun bayyana ra'ayoyi mabanbanta kan janyewa daga tsayawa takara da shugaba Joe Biden ya yi, inda wasu ke gani ya yi abin da wasu kasashe za su yi koyi da shi.

Shugaba Joe Biden na Amurka ya janye kamfe din neman zabe a wa'adi na biyu yana mai kawo damuwa kan karfin tunaninsa da damar da zai iya samun nasara akan Donald Trump.

A cikin sanarwar da ya wallafa a shafinsa na X, Biden ya tabbatar da cewa zai ci gaba da gudanar da mulki a matsayinsa na shugaban kasa har karshen wa'adinsa a watan Janairu na shekara mai zuwa.

Farfesa Ghali Sharrif shugaban tsangayar Siyasa a Jami'ar Abuja ya yi nazari kan matakin da Joe Biden ya dauka inda ya ce Shugaba Biden dan siyasa ne kuma Jam'iyyarsa ta fahimci cewa farin jinin Biden ya ragu musamman bayan mahawararsa da tsohon Shugaban Amurka Donald Trump.

Shi kuwa masanin siyasa da diflomasiyar kasa da kasa kuma malami a Jami'ar Abuja Dr. Farouk Bibi Farouk ya yi bayani cewa matakin Biden abin yabawa ne, kuma ya nuna cewa siyasar Amurka musamman ta dimokradiya tana so ta nuna isa da bajinta na cewa kowane irin mutum yana iya samun dama na tsayawa takara.

Farouk ya kara da cewa, akwai kuma alamu na cewa yanzu za a yi siyasar Amurka da kowane jinsi, ganin cewa an ba bakar fata dama a lokacin da aka zabi Barack Obama, wannan ya na nuna cewa za a ci gaba da samun irin wannan guguwar sauyi a siyasar kasar.

Ita ma 'yar siyasa kuma 'yar gwagwarmayar kwato wa mata yanci Hajiya Mariya Ibramin Baba ta ce labarin da ya zo da dumi dumin sa cewa Shugaba Biden ya dora Kamala Harris a matsayin 'yar takarar shugabancin Amurka ya yi wa mata dadi sosai, domin wannan ya nuna cewa dole a yi da mata a dukanin fanonin siyasar Amurka. Mariya ta ce Kamala ta nuna bajinta a aikin ta, domin Biden ya sha bar mata aikin kasar kuma ta rike da kyau. Mariya ta ce mata suna murna sosai.

Shi ma shugaban kungiyar CISLAC mai sa ido a harkokin Majalisu Auwal Musa Rafsanjani ya ce wannan mataki ya yi kyau kwarai da gaske, kuma yana mai fata kasashe da ke koyi da dimokradiya na kasar Amurka irin su Najeriya su yi koyi da matakin da Biden ya dauka, domin zai kara inganta dimokradiya musamman a kasashe masu tasowa.

Saurari cikakken rahot dag Medina Dauda:

Abin Da Kwararru Ke Cewa Kan Janyewar Biden Daga Takarar Shugaban Kasa
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:23 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG