Wannan shine karon farko da aka samu irin wannan hari tun cikin karshen watan Agusta, lokacin da wani dan kunar bakin wake na kungiyar IS ya kai hari a lardin Khorasan da ya kashe kusan mutane 200, ciki har da ma’aikatan sojan Amurka 13 a kusa da filin saukar jirage na Kabul.
Sai dai nan da nan babu wata kungiyar da ta dauki alhakin kai harin na jiya Lahadi a kan masallacin Eid Gah dake tsakiyar birnin kana ya auna taron jama’ar dake gudanar da addu’o’I na musamman ga mahaifiyar babban kakakin Taliban Zabihullah Mujahid da ta rasu kwanan nan.
Mai magana da yawun Taliban a Qatar Suhail Shaheen ya ce Mujahid na cikin koshin lafiya tare da wasu abokan aikinsa, saboda bam din ya tashi ne a kusa da inda suke.
Wani dan kungiyar Taliban Hamidullah, ya ce yana tazarar ‘yan mitoci uku ne kacal daga inda dan kunar bakin waken ya kai harin a kusa da masallacin.
Reshen kungiyar IS ta Khorasan, dake da tungarta a Afghanistan, da aka fi saninta da ISIS-K, ta dauki alhakin kai wasu jerin hare hare da dama a lardunan gabashin kasar da suka hada da Nangahar da Kunar a makon da ya gabata, da suka kashe fararen hula da dama da mayakan Taliban.