WASHINGTON, D. - Babu wanda ya dauki alhakin kai harin na ranar Lahadi, wanda kuma ya raunata kusan mutane 200. 'Yan sanda sun ce binciken farko da suka gudanar ya nuna cewa kungiyar da ke da alaka da kungiyar IS na iya daukar alhakin hakan.
Wadanda aka kashe din dai sun halarci wani gangami ne da jam’iyyar Jamiat Ulema Islam ta shirya, karkashin jagorancin malamin addini kuma dan siyasa Fazlur Rehman. Bai halarci gangamin ba, wanda aka gudanar a karkashin wata babbar tanti da ke kusa da wata kasuwa a Bajur, gundumar da ke lardin Khyber Pakhtunkhwa mai iyaka da Afghanistan.
An dai binne wadanda harin bam din ya rutsa da su a Bajur a yau Litinin.
A kuma ranar ta Litinin, 'yan sanda suka dauki bayanan wasu daga cikin wadanda suka jikkata a wani asibiti a Khar, babban garin Bajur. Feroz Jamal, Ministan yada labaran lardin, ya ce 'yan sanda suna "binciken wannan harin ta kowane fanni."
-AP
Dandalin Mu Tattauna