Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harin Da Aka Kai Masallaci A Maiduguri


Mutane cikin masallacin da bom ya fashe a Maiduguri Najeriya, 23 Oktoba, 2015.
Mutane cikin masallacin da bom ya fashe a Maiduguri Najeriya, 23 Oktoba, 2015.

A kalla mutane takwas aka kashe a wani harin kunar bakin wake a Maiduguri, Najeriya. Kimanin 20 kuma suka ji raunuka a fashewar da ta auku lokacin sallar Asuba.

Rahotanni sun ce nakiyoyi biyu sun tashi a cikin masallacin dake Jiddari Polo a harin bom na baya bayan nan a babban birnin jihar Borno cibiyar mayakan kungiyar Boko Haram.

Ranar jumma’a da ta gabata, a kalla ‘yan kunar bakin wake uku suka tarwatsa kansu a bayan garin Maiduguri, suka kashe a kalla mutane hudu ‘yan sa’oi bayan wani hari da ‘yan kunar bakin wake biyu suka kai a babban birnin kasar da ya kashe mutane 37.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG