Gwamnati ta haramta ayyukan kungiyar likitocin a watan Disambar da ya gabata. Bayan zargin kungiyar da tallafawa kungiyoyi masu dauke da makamai wadanda ba na gwamnati ba da ta saba bayyanawa a matsayin 'yan ta'adda. Kungiyar likitocin na Doctors Without Borders ta musanta zargin.
Tana kira ga gwamnati da ta fifita bukatun aikin jinya na dubun-dubatar 'yan ƙasa waɗanda ke buƙatar taimakon likita don rayuwa. Emmanuel Lampaert shine Mai Gudanar da Ayyuka na Kungiyar likitocin kasa da kasa ta agaji a Afirka ta Tsakiya.
Ya ce abin takaici ne yadda hukumomi za su dakatar da ayyukan jinya ga dubun-dubatar mutanen da ke bukatar kiwon lafiya. Lampaert ya fadawa wakilin Muryar Amurka Peter Clottey cewa manyan jami’an kungiyar sa zasu ci gaba da tattaunawa da hukumomi don dage takunkumin.