WASHINGTON, D. C. - An yi harbe-harben ne a kusa da karshen bikin wasan kwallon Super Bowl na Kansas City Chiefs's wanda ya firgita dimbin magoya bayan kungiyar kwallon zari ruga.
Harin na ranar Laraba a tashar Union ya faru ne duk da kasancewar jami’an ‘yan sanda sama da 800 a cikin ginin da kuma kusa da wurin, ciki har da saman gine-ginen da ke kusa da wurin, in ji magajin garin Quinton Lucas, wanda ya halarci bikin tare da matarsa da mahaifiyarsa kuma suma suka gudu don tsira a lokacin da harbe-harben suka tashi.
Lucas ya kara da cewa “Fareti, gangami, makarantu, wajen kallon fina-finai. Da alama kusan babu wani wuri da ke da tsaro,”
An tsare mutane uku tare da kwato bindigogi, in ji Shugabar ‘yan sanda Stacey Graves a wani taron manema labarai da yammacin jiya. Ta ce 'yan sanda na ci gaba da tattara abubuwan da suka faru kuma ba su bayar da cikakken bayani game da wadanda aka tsare ba ko kuma wata manufa aikata wannan tashin hankali ba.
“Ina matukar bacın rai da abin da ya faru a yau. Mutanen da suka zo wannan bikin ya kamata su yi tsammanin samun yanayi mai aminci da cikakken tsaro,” in ji Graves.
Wannan dai shi ne bikin wasanni na baya-bayan nan da aka yi a Amurka da ake fama da tashin hankali, bayan harbin da ya raunata mutane da dama a bara a garin Denver, jihar Colorado, bayan gasar Nuggets’ NBA, da kuma harbin bindiga a bara a wurin ajiye motoci kusa da gasar tseren duniya da fareti na Texas Rangers.
-AP
Dandalin Mu Tattauna