Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

​An Kaiwa Sarakunan Borno Hari; Daya Ya Rasu


‘Yan Boko Haram sun budewa wannan motar haya wuta lokaci da yake tafiya tsakanin Konduga da Bama a makonin baya.
‘Yan Boko Haram sun budewa wannan motar haya wuta lokaci da yake tafiya tsakanin Konduga da Bama a makonin baya.

Majiyoyi da dama daga Najeriya sun tabbatar cewa ‘yan bindiga sun sace Sarkin Uba, Alhaji Ali Ismail Mamza, a lokacin da aka kaiwa jerin gwanon motocinsu hari tare da Sarkin Gwoza da Sarkin Askira Alhaji Abdullahi Ibn Muhammad Askirama.

Rahotanni sunce Sarkin Gwoza Alhaji Idris Timta ya rasu sakamakon wannan hari, Sarkin Askira kuma ya kubuta a lokacinda motarshi dake bayan na sauran sarakunan ta juya, ta koma baya.

Rahotanni sunce ‘yan bindiga su sama da 100 sunyi kwanton bauna ne a kauyen Zur dake kan hanyar Garkida zuwa Biu, inda nan take suka budewa motocin sarakunan wuta. ‘Yan bindigan wadanda ke cikin motocin “Hilux” da babura sunyi shige da mayakan Boko Haram wadanda suka addabi yankin arewacin Najeriya. Ko da yake ‘yan banga da sauran jami’an tsaron dake tare da sarakunan sun mayar da martani.

Sarkin Mubi Abubakar Isa Amadu yayi sa’ar wucewa ba tare da matsala ba.

Sarakunan na kan hanyarsu ne zuwa garin Gombe, domin hallartar jana’izar Sarkin Gombe, Alhaji Shehu Usman.
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG