Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kaiwa 'Yan Tawayen Syria Mummunan Hari a Masallaci


Mutane 42 ne suka mutu kana wasu da dama suka samu rauni, sakamakon harin da aka kaiwa ‘yan tawaye a wani masallacin da yan tawayen ke rike dashi a arewacin Syria, kamar yadda kungiyar nan da ake kira da turaci Syrian Observatory for Human right ke cewa.

Masu aikin bada agajin gaggawa, da masu kare fararen hula duka dake kasar ta Syria suka ce tuni suka isa wannan wuri domin taimaka wa wadanda wannan lamari ya rutsa dasu jiya alhamis a jeenah wanda ke yankin gundumar Aleppo.

Masu bada wannan agajin farko da suka isa wannan wurin sunce a kalla mutane 20 suka mutu nan take.

Kungiyar mai hedikwata a Landan tace masallacin da wannan lamari ya faru yana cike ne da masu ibada, wadanda galibi suna sallar Isshai ne, kungiyar tace sama da mutane 100 suka samu rauni, yayin da wasu da dama suna cikin kura kuzan ginin masallacin da aka kaiwa hari.

Sai dai kungiyar tace har yanzu ta kasa tantance wani jirgin ne yakai wannan harin.

A lokuttan baya dai sojojin Syria da na Rasha sune suke kai hari da jirgin sama a Idlib da kuma gundumar Aleppo a cikin shekaru 6 da aka kwashe ana wannan yakin basasan.

Sai dai kuma ko baya ga jiragen Syria dana Rasha a kwai tawagar sojojin saman Amurka da ke aiki a wannan wuri.

Wannan harin yazo ne kwana daya bayan wani harin kunar bakin wake da aka kai a fadar gwamnatin kasar na Damascus, wanda yayi dalilin mutuwar mutane 30.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG